Hukumar Haraji Ta Kasa FIRS Ta Umurci Bankuna Da Su Fara Cire Harajin Kashi 10%
Hukumar Haraji Ta Kasa FIRS Ta Umurci Bankuna Da Su Fara Cire Harajin Kashi 10%
Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta bayar da sabon umarni ga bankuna, dillalan hannayen jari, da sauran cibiyoyin kuɗi su fara cire harajin kashi 10% (Withholding Tax) daga ribar da ake samu a takardun bashi na ɗan gajeren lokaci (short-term securities).
FIRS ta ce wannan mataki yana cikin ƙoƙarin gwamnati na ƙara samun kuɗaɗen shiga, da kuma tabbatar da cewa duk masu zuba jari suna biyan haraji bisa doka.
Hakan zai shafi duk masu riba daga Treasury Bills, Bonds, da sauran takardun bashi na gwamnati ko na kamfanoni.
Nagarifmradio




